Surat Al-Fatihah

سُورَةُ ٱلْفَاتِحَةِ

Makkiyya · aya 7 · Juz'i 1

Haddace Surat Al-FatihahKaranta da murya, Shamsa ta saurara, ta nuna kalmar da ka tsallake ko ka yi kuskure a ciki. Da rubutun Boko, kyauta.

Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ ﴿١﴾

1. Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلْعَٰلَمِينَ ﴿٢﴾

2. Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;

ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ ﴿٣﴾

3. Mai rahama, Mai jin ƙai;

مَٰلِكِ يَوْمِ ٱلدِّينِ ﴿٤﴾

4. Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.

إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ ﴿٥﴾

5. Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa.

ٱهْدِنَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلْمُسْتَقِيمَ ﴿٦﴾

6. Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.

صِرَٰطَ ٱلَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ ٱلْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا ٱلضَّآلِّينَ ﴿٧﴾

7. Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.

Fassara © Abubakar Mahmoud Gumi. Rubutun Larabci (Uthmani): Shirin Tanzil.

A manhajar Shamsa za ku iya sauraron kowace sura, ku yi alama a inda kuka tsaya, ku kuma karanta ba tare da intanet ba.