Addu'o'i Daga Alƙur'ani
Addu'o'i daga Alƙur'ani da Larabcin mushafi. Fassarar ta Abubakar Mahmoud Gumi ce; an rubuta sura da aya a ƙarƙashin kowace addu'a.
Alheri a duniya da Lahira
رَبَّنَآ ءَاتِنَا فِى ٱلدُّنْيَا حَسَنَةًۭ وَفِى ٱلْءَاخِرَةِ حَسَنَةًۭ وَقِنَا عَذَابَ ٱلنَّارِ ﴿٢٠١﴾
Rabbana atina fid-dunya hasanatan wa fil-akhirati hasanatan wa qina 'adhaban-nar
Yã Ubangijinmu! Ka bã mu mai kyau a cikin dũniya da mai kyau a cikin Lãhira, kuma Ka tsare mana azãbar Wuta!
Addu'ar da Annabi (S.A.W.) ya fi yawan yi; a wannan ruwayar tana farawa da "Allahumma" (Bukhari 6389).
Alƙur'ani, Al-Baqarah 2:201 · Bukhari 6389 · Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi
Kada Ka kama mu
رَبَّنَا لَا تُؤَاخِذْنَآ إِن نَّسِينَآ أَوْ أَخْطَأْنَا ۚ رَبَّنَا وَلَا تَحْمِلْ عَلَيْنَآ إِصْرًۭا كَمَا حَمَلْتَهُۥ عَلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِنَا ۚ رَبَّنَا وَلَا تُحَمِّلْنَا مَا لَا طَاقَةَ لَنَا بِهِۦ ۖ وَٱعْفُ عَنَّا وَٱغْفِرْ لَنَا وَٱرْحَمْنَآ ۚ أَنتَ مَوْلَىٰنَا فَٱنصُرْنَا عَلَى ٱلْقَوْمِ ٱلْكَٰفِرِينَ ﴿٢٨٦﴾
Rabbana la tu'akhidhna in nasina aw akhta'na, rabbana wa la tahmil 'alayna isran kama hamaltahu 'alalladhina min qablina, rabbana wa la tuhammilna ma la taqata lana bih, wa'fu 'anna waghfir lana warhamna, anta mawlana fansurna 'alal-qawmil-kafirin
Yã Ubangijinmu! Kada Ka kãmã mu, idan mun yi mantuwa, ko kuma mun yi kuskure. Yã Ubangijinmu! Kuma kada Ka aza nauyi a kanmu, kamar yadda Ka aza shi a kan waɗanda suke a gabãninmu. Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanya mu ɗaukar abin da bãbu ĩko gare mu da shi. Kuma Ka yãfe daga gare mu, kuma Ka gãfarta mana, kuma Ka yi jin ƙai gare mu. Kai ne Majibincinmu, sabõda haka Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai.
Alƙur'ani, Al-Baqarah 2:286 · Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi
Ka tabbatar da zukatanmu
رَبَّنَا لَا تُزِغْ قُلُوبَنَا بَعْدَ إِذْ هَدَيْتَنَا وَهَبْ لَنَا مِن لَّدُنكَ رَحْمَةً ۚ إِنَّكَ أَنتَ ٱلْوَهَّابُ ﴿٨﴾
Rabbana la tuzigh qulubana ba'da idh hadaytana wa hab lana min ladunka rahmah, innaka antal-Wahhab
Yã Ubangijinmu! Kada Ka karkatar da zukãtanmu bãyan har Kã shiryar da mu, kuma Ka bã mu rahama daga gunKa. Lalle ne, Kai, Kai ne Mai yawan kyauta.
Alƙur'ani, Ali 'Imran 3:8 · Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi
Addu'ar Adamu da Hauwa'u
رَبَّنَا ظَلَمْنَآ أَنفُسَنَا وَإِن لَّمْ تَغْفِرْ لَنَا وَتَرْحَمْنَا لَنَكُونَنَّ مِنَ ٱلْخَٰسِرِينَ ﴿٢٣﴾
Rabbana zalamna anfusana wa in lam taghfir lana wa tarhamna lanakunanna minal-khasirin
Ya Ubangijinmu! Mun zãlunci kanmu. Kuma idan ba Ka gãfarta mana ba, kuma Ka yi mana rahama, haƙĩƙa, Munã kasancẽwa daga mãsu hasãra.
Adamu da Hauwa'u ne suka yi ta bayan kuskurensu, suna neman gafara.
Alƙur'ani, Al-A'raf 7:23 · Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi
Ka sa in tsayar da sallah
رَبِّ ٱجْعَلْنِى مُقِيمَ ٱلصَّلَوٰةِ وَمِن ذُرِّيَّتِى ۚ رَبَّنَا وَتَقَبَّلْ دُعَآءِ ﴿٤٠﴾ رَبَّنَا ٱغْفِرْ لِى وَلِوَٰلِدَىَّ وَلِلْمُؤْمِنِينَ يَوْمَ يَقُومُ ٱلْحِسَابُ ﴿٤١﴾
Rabbij-'alni muqimas-salati wa min dhurriyyati, rabbana wa taqabbal du'a'. Rabbanaghfir li wa li-walidayya wa lil-mu'minina yawma yaqumul-hisab
Yã Ubangijina! Ka sanyã ni mai tsayar da salla. Kuma daga zũriyyata. Yã Ubangijinmu! Kuma Ka karɓi addu'ata. Yã Ubangijinmu! Ka yi gãfara gare ni, kuma ga mahaifãna, kuma da mũminai, a rãnar da hisãbi yake tsayãwa.
Addu'ar Annabi Ibrahim ce. Aya ta biyu daga cikinta ana yawan karanta ta a zaman ƙarshe na sallah.
Alƙur'ani, Ibrahim 14:40-41 · Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi
Addu'a ga iyaye
رَبِّ ٱرْحَمْهُمَا كَمَا رَبَّيَانِى صَغِيرًۭا ﴿٢٤﴾
Rabbir-hamhuma kama rabbayani saghira
Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda suka yi rẽnõna, ina ƙarami.
Alƙur'ani, Al-Isra 17:24 · Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi
Ka buɗa mini ƙirjina
رَبِّ ٱشْرَحْ لِى صَدْرِى ﴿٢٥﴾ وَيَسِّرْ لِىٓ أَمْرِى ﴿٢٦﴾ وَٱحْلُلْ عُقْدَةًۭ مِّن لِّسَانِى ﴿٢٧﴾ يَفْقَهُوا۟ قَوْلِى ﴿٢٨﴾
Rabbish-rah li sadri, wa yassir li amri, wahlul 'uqdatan min lisani, yafqahu qawli
Ya Ubangiji! Ka buɗa mini, ƙirjĩna. Kuma ka sauƙaƙe mini al'amarĩna. Kuma Ka warware mini wani ƙulli daga harshẽna. Su fahimci maganãta.
Addu'ar Annabi Musa ce kafin aikensa; ana yawan yin ta kafin karatu ko kafin magana.
Alƙur'ani, Ta-Ha 20:25-28 · Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi
Ka ƙara mini ilimi
رَبِّ زِدْنِى عِلْمًۭا ﴿١١٤﴾
Rabbi zidni 'ilma
Yã Ubangiji! Ka ƙãra mini ilmi.
Alƙur'ani, Ta-Ha 20:114 · Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi
Addu'ar Annabi Yunusa
لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنتَ سُبْحَٰنَكَ إِنِّى كُنتُ مِنَ ٱلظَّٰلِمِينَ ﴿٨٧﴾
La ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz-zalimin
Bãbu abĩn bautãwa fãce Kai. Tsarki ya tabbata a gare Ka. Lalle ne nĩ, na kasance daga azzãlumai.
Annabi Yunusa ne ya yi kira da ita daga cikin cikin kifi. Babu wani Musulmi da zai roƙi wani abu da ita face Allah Ya amsa masa (Tirmizi 3505).
Alƙur'ani, Al-Anbiya 21:87 · Tirmizi 3505 · Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi
Addu'ar Annabi Ayyuba
أَنِّى مَسَّنِىَ ٱلضُّرُّ وَأَنتَ أَرْحَمُ ٱلرَّٰحِمِينَ ﴿٨٣﴾
Anni massaniyad-durru wa anta arhamur-rahimin
Lalle nĩ, cũta ta shãfe ni, alhãli kuwa Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama.
Annabi Ayyuba ne ya yi ta a lokacin doguwar rashin lafiyarsa.
Alƙur'ani, Al-Anbiya 21:83 · Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi
Allah Ya isar mana
حَسْبُنَا ٱللَّهُ وَنِعْمَ ٱلْوَكِيلُ ﴿١٧٣﴾
Hasbunallahu wa ni'mal-wakil
Mai isarmu Allah ne kuma mãdalla da wakili Shĩ.
Annabi Ibrahim ne ya faɗe ta lokacin da aka jefa shi cikin wuta, haka kuma Annabi (S.A.W.) lokacin da aka gaya masa cewa runduna ta taru domin yaƙarsa (Bukhari 4563).
Alƙur'ani, Ali 'Imran 3:173 · Bukhari 4563 · Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi
Ina buƙatar duk wani alheri
رَبِّ إِنِّى لِمَآ أَنزَلْتَ إِلَىَّ مِنْ خَيْرٍۢ فَقِيرٌۭ ﴿٢٤﴾
Rabbi inni lima anzalta ilayya min khayrin faqir
Yã Ubangijĩna! Lalle ne, ga abin da Ka saukar zuwa gare ni na alhẽri ni mai bukãta ne.
Annabi Musa ne ya faɗe ta a Madyana, baƙo ne kuma ba shi da komai.
Alƙur'ani, Al-Qasas 28:24 · Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi
Ka yi gafara Ka yi rahama
رَبِّ ٱغْفِرْ وَٱرْحَمْ وَأَنتَ خَيْرُ ٱلرَّٰحِمِينَ ﴿١١٨﴾
Rabbighfir warham wa anta khayrur-rahimin
Yã Ubangijina! Ka yi gãfara, Ka yi rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu rahama.
Alƙur'ani, Al-Mu'minun 23:118 · Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi
Addu'a ga mata ko miji da 'ya'ya
رَبَّنَا هَبْ لَنَا مِنْ أَزْوَٰجِنَا وَذُرِّيَّٰتِنَا قُرَّةَ أَعْيُنٍۢ وَٱجْعَلْنَا لِلْمُتَّقِينَ إِمَامًا ﴿٧٤﴾
Rabbana hab lana min azwajina wa dhurriyyatina qurrata a'yunin waj'alna lil-muttaqina imama
Yã Ubangijinmu! Ka bã mu sanyin idãnu daga mãtanmu da zũriyarmu, kuma Ka sanya mu shũgabanni ga mãsu taƙawa.
Alƙur'ani, Al-Furqan 25:74 · Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi
Addu'a ga waɗanda suka riga mu
رَبَّنَا ٱغْفِرْ لَنَا وَلِإِخْوَٰنِنَا ٱلَّذِينَ سَبَقُونَا بِٱلْإِيمَٰنِ وَلَا تَجْعَلْ فِى قُلُوبِنَا غِلًّۭا لِّلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ رَبَّنَآ إِنَّكَ رَءُوفٌۭ رَّحِيمٌ ﴿١٠﴾
Rabbanaghfir lana wa li-ikhwaninalladhina sabaquna bil-iman, wa la taj'al fi qulubina ghillan lilladhina amanu, rabbana innaka Ra'ufun Rahim
Yã Ubangijinmu! Ka yi gãfara a gare mu, kuma ga 'yan'uwanmu, waɗanda da suka riga mu yin ĩmãni, kada Ka sanya wani ƙulli a cikin zukãtanmu ga waɗanda suka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Lalle Kai ne Mai tausayi, Mai jin ƙai.
Alƙur'ani, Al-Hashr 59:10 · Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi