Surat At-Takathur

سُورَةُ التَّكَاثُرِ

Makkiyya · aya 8 · Juz'i 30

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

Haddace Surat At-TakathurKaranta da murya, Shamsa ta saurara, ta nuna kalmar da ka tsallake ko ka yi kuskure a ciki. Da rubutun Boko, kyauta.

Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi

أَلْهَىٰكُمُ ٱلتَّكَاثُرُ ﴿١﴾

1. Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (dagaibada mai amfaninku).

حَتَّىٰ زُرْتُمُ ٱلْمَقَابِرَ ﴿٢﴾

2. Har kuka ziyarci kaburbura.

كَلَّا سَوْفَ تَعْلَمُونَ ﴿٣﴾

3. A'aha! (Nan gaba) zã ku sani.

ثُمَّ كَلَّا سَوْفَ تَعْلَمُونَ ﴿٤﴾

4. Sa'an nan, tabbas, zã ku sani.

كَلَّا لَوْ تَعْلَمُونَ عِلْمَ ٱلْيَقِينِ ﴿٥﴾

5. Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni.

لَتَرَوُنَّ ٱلْجَحِيمَ ﴿٦﴾

6. Lalle ne da kuna ganin Jahĩm.

ثُمَّ لَتَرَوُنَّهَا عَيْنَ ٱلْيَقِينِ ﴿٧﴾

7. Sa'an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane.

ثُمَّ لَتُسْـَٔلُنَّ يَوْمَئِذٍ عَنِ ٱلنَّعِيمِ ﴿٨﴾

8. Sa'an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku).

Fassara © Abubakar Mahmoud Gumi. Rubutun Larabci (Uthmani): Shirin Tanzil.

A manhajar Shamsa za ku iya sauraron kowace sura, ku yi alama a inda kuka tsaya, ku kuma karanta ba tare da intanet ba.