Surat Ash-Sharh

سُورَةُ الشَّرۡحِ

Makkiyya · aya 8 · Juz'i 30

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

Haddace Surat Ash-SharhKaranta da murya, Shamsa ta saurara, ta nuna kalmar da ka tsallake ko ka yi kuskure a ciki. Da rubutun Boko, kyauta.

Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi

أَلَمْ نَشْرَحْ لَكَ صَدْرَكَ ﴿١﴾

1. Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)?

وَوَضَعْنَا عَنكَ وِزْرَكَ ﴿٢﴾

2. Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe.

ٱلَّذِىٓ أَنقَضَ ظَهْرَكَ ﴿٣﴾

3. Wanda ya nauyayi bãyanka?

وَرَفَعْنَا لَكَ ذِكْرَكَ ﴿٤﴾

4. Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka?

فَإِنَّ مَعَ ٱلْعُسْرِ يُسْرًا ﴿٥﴾

5. To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.

إِنَّ مَعَ ٱلْعُسْرِ يُسْرًۭا ﴿٦﴾

6. Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.

فَإِذَا فَرَغْتَ فَٱنصَبْ ﴿٧﴾

7. Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah).

وَإِلَىٰ رَبِّكَ فَٱرْغَب ﴿٨﴾

8. Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi.

Fassara © Abubakar Mahmoud Gumi. Rubutun Larabci (Uthmani): Shirin Tanzil.

A manhajar Shamsa za ku iya sauraron kowace sura, ku yi alama a inda kuka tsaya, ku kuma karanta ba tare da intanet ba.