Surat Al-Ma'un
سُورَةُ المَاعُونِ
Makkiyya · aya 7 · Juz'i 30
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi
أَرَءَيْتَ ٱلَّذِى يُكَذِّبُ بِٱلدِّينِ ﴿١﴾
1. Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako?
فَذَٰلِكَ ٱلَّذِى يَدُعُّ ٱلْيَتِيمَ ﴿٢﴾
2. To, wannan shi ne ke tunkue marãya (daga haƙƙinsa).
وَلَا يَحُضُّ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلْمِسْكِينِ ﴿٣﴾
3. Kuma bã ya kwaaitarwa bisa bãyar da abinci ga matalauci.
فَوَيْلٌۭ لِّلْمُصَلِّينَ ﴿٤﴾
4. To, bone yã tabbata ga masallata.
ٱلَّذِينَ هُمْ عَن صَلَاتِهِمْ سَاهُونَ ﴿٥﴾
5. Waɗanda suke masu shagala daga sallarsu.
ٱلَّذِينَ هُمْ يُرَآءُونَ ﴿٦﴾
6. Waɗanda suke yin riya (ga ayyukansu)
وَيَمْنَعُونَ ٱلْمَاعُونَ ﴿٧﴾
7. Kuma suna hana taimako.
Fassara © Abubakar Mahmoud Gumi. Rubutun Larabci (Uthmani): Shirin Tanzil.
A manhajar Shamsa za ku iya sauraron kowace sura, ku yi alama a inda kuka tsaya, ku kuma karanta ba tare da intanet ba.