Surat An-Nas
سُورَةُ النَّاسِ
Makkiyya · aya 6 · Juz'i 30
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
Fassara: Abubakar Mahmoud Gumi
قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلنَّاسِ ﴿١﴾
1. Ka ce "Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne."
مَلِكِ ٱلنَّاسِ ﴿٢﴾
2. "Mamallakin mutane."
إِلَٰهِ ٱلنَّاسِ ﴿٣﴾
3. "Abin bautãwar mutãne."
مِن شَرِّ ٱلْوَسْوَاسِ ٱلْخَنَّاسِ ﴿٤﴾
4. "Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa."
ٱلَّذِى يُوَسْوِسُ فِى صُدُورِ ٱلنَّاسِ ﴿٥﴾
5. "Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane."
مِنَ ٱلْجِنَّةِ وَٱلنَّاسِ ﴿٦﴾
6. "Daga aljannu da mutane."
Fassara © Abubakar Mahmoud Gumi. Rubutun Larabci (Uthmani): Shirin Tanzil.
A manhajar Shamsa za ku iya sauraron kowace sura, ku yi alama a inda kuka tsaya, ku kuma karanta ba tare da intanet ba.